Mutum na iya manta damuwarsa Zuwa wani lokaci bakin ciki kan gushe Damuwata, kamar dusar kankara, ta ki ta gushe Ta ki gushewa, ta ki gushewa Ba za ta narke cikin yanayin gumi ba A tsakar rana cikin bazara Na hakikance, daga damuwata ba zan Taba samun tsira ba.
Yusuf Adamu. Fassara, 2015